source avatarSir salim.org

مشاركة

Hadisi na Shida a cikin Arba'una Hadisan Imam Nawawi عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي الله عنهما، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ ﷺ يَقُولُ: إِنَّ الْحَلَالَ بَيِّنٌ، وَإِنَّ الْحَرَامَ بَيِّنٌ، وَبَيْنَهُمَا أُمُورٌ مُشْتَبِهَاتٌ لَا يَعْلَمُهُنَّ كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ، فَمَنِ اتَّقَى الشُّبُهَاتِ اسْتَبْرَأَ لِدِينِهِ وَعِرْضِهِ، وَمَنْ وَقَعَ فِي الشُّبُهَاتِ وَقَعَ فِي الْحَرَامِ، كَالرَّاعِي يَرْعَى حَوْلَ الْحِمَى يُوشِكُ أَنْ يَرْتَعَ فِيهِ، أَلَا وَإِنَّ لِكُلِّ مَلِكٍ حِمًى، أَلَا وَإِنَّ حِمَى اللَّهِ مَحَارِمُهُ، أَلَا وَإِنَّ فِي الْجَسَدِ مُضْغَةً إِذَا صَلَحَتْ صَلَحَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، وَإِذَا فَسَدَتْ فَسَدَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، أَلَا وَهِيَ الْقَلْبُ. رَوَاهُ الْبُخَارِيُّ وَمُسْلِمٌ. Daga Abu Abdullahi Nu'uman ɗan Bashir (RA), ya ce: Na ji Manzon Allah ﷺ yana cewa: Lallai halal a bayyane yake, kuma haram ma a bayyane yake. A tsakaninsu akwai wasu abubuwa masu kama da juna (shubuhohi) waɗanda mutane da yawa ba su san hukuncinsu ba. Duk wanda ya nisanci abubuwan da ake shakku a kansu, to ya tsarkake addininsa da mutuncinsa. Wanda kuma ya faɗa cikin abubuwan da ake shakku a kansu, to yana iya faɗawa cikin haram, kamar makiyayi ne da yake kiwo a kusa da iyakar wani fili da aka killace, kusan dabbobinsa su shiga cikinsa. Ku saurara, Kowanne sarki yana da filin da ya killace. Ku saurara! Abin da Allah Ya killace shi ne abubuwan da Ya haramta. Ku saurara! A cikin jiki akwai wani ɗan nama, idan ya gyaru, dukkan jiki ya gyaru; idan kuma ya lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! Wannan shi ne zuciya." An rawaito hadisin daga Bukhari da Muslim.

إخلاء المسؤولية: قد تكون المعلومات الواردة في هذه الصفحة قد حصلت عليها من أطراف ثالثة ولا تعكس بالضرورة وجهات نظر أو آراء KuCoin. يُقدّم هذا المحتوى لأغراض إعلامية عامة فقط ، دون أي تمثيل أو ضمان من أي نوع ، ولا يجوز تفسيره على أنه مشورة مالية أو استثمارية. لن تكون KuCoin مسؤولة عن أي أخطاء أو سهو ، أو عن أي نتائج ناتجة عن استخدام هذه المعلومات. يمكن أن تكون الاستثمارات في الأصول الرقمية محفوفة بالمخاطر. يرجى تقييم مخاطر المنتج بعناية وتحملك للمخاطر بناء على ظروفك المالية الخاصة. لمزيد من المعلومات، يرجى الرجوع إلى شروط الاستخدام واخلاء المسؤولية.